• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI YA ZIYARCI BORNO

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno don karfafa guiwar jami’an tsaro.

Shugaban ya yi wa sojoji a rundunar yaki dan’yan boko haram cajin batur don su kara himma wajen murkushe ‘yan ta’addan.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin tabbatar da cewa madugun ‘yan ta’addan Abubakar Shekau ya riga mu gidan gaskiya da gaske ba kamar yanda a baya a kan ba da labarin shekawar sa barzahu amma sai ya fito ya ce ga shi nan a raye.

A lokacin xiyarar, shugaban ya kaddamar da wasu aiyuka da su ka hada da gidaje ga wadanda su ka rasa matsugunai a sanadiyyar fitianr ta’addanci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
47 thoughts on “SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI YA ZIYARCI BORNO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.