• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI YA GANA DA JANAR DANJUMA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Janar Theophilus Danjuma mai ritaya a fadar Aso Rock.

Janar Danjuma wanda tsohon ministan tsaro ne, ya taka rawa a gwamnatocin soja musamman bayan kawar da Janar Aguiyi Ironsi inda gwamnatin Janar Gowon ta hau karaga na tsawon shekaru 9 da ya hada da zamanin yakin basasa.

Ba wani abun mamaki ganawar a matsayin Janar Danjuma na tsohon babban hafsa a soja .

Masu sharhi na ganin ganawar da ta zama kusan ta biyu a bana, na da nasaba da lamuran tsaro.

Danjuma wanda dan Takum ne a jihar Taraba kan yi maganganun da kan yi ci karo da muradin gwamnatin Buhari ko ma jami’an sojoji da ya zarga da hada kai wajen fitinar kabilanci a jihar Taraba.

Masu sharhi na ganin ba don matsayin Danjuma, da wani ke irin maganganun sa, da ya shiga komar jami’an tsaro musamman samun gaiyata daga DSS.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI YA GANA DA JANAR DANJUMA”
  1. Superb blog! Do you have any helpful hints for aspiring writers?

    I’m planning to start my own blog soon but I’m a little lost
    on everything. Would you advise starting with
    a free platform like WordPress or go for a paid option? There are so many options out there that I’m completely confused ..
    Any ideas? Thank you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.