• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN MAKARANTAR YARA A KANO YA KASHE DALIBAR SA

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta cafke shugaban wata makaranta mai zaman kan ta a Kano “NOBLE KIDS’ mai suna Abdulmalik Tanko don sacewa da kashe dalibar sa Hanifa Abubakar mai shekaru 5.
Binciken ‘yan sanda ya gano cewa malamin tun farko shi ya sace dalibar ta sa inda ya kai ta gidan sa da neman kudin fansa Naira miliyan 6.
Tanko da kansa ya shaidawa ‘yan sanda cewa Hanifa ta gane shi don haka ya shayar da ita guba ta mutu sannan ya sa wani mai suna Hashim Isyaku ya dauki yarinyar ya kai ta harabar makarantar ya bunne ta.
Majiya daga gidan su yarinyar ta baiyana cewa malamin na daya daga mutanen farko da su ka zo su ka jajanta mu su kan sace Hanifa kuma ya na mai zubar da hawaye.
Tuni an tono Hanifa a ka kai ta asibiti inda likita ya tabbatar rai ya yi halin sa daga nan a ka mika ta wajen iyayen ta don jana’iza bisa tanadin Islama.
Bayan kammala bincike ne,za a gurfanar da Tanko gaban kotu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.