Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmed Lawan na tsaka mai wuya wajen neman tikitin dawowa majalisar dattawa.
Lawan dai wanda ya tafi takarar shugaban kasa amma bai samu nasara ba, ya tarar da Bashir Machina ya lashe zaben tikitin kujerar sa ta majalisar dattawa, kuma rahotanni sun nuna Machina ya na tsayin dakar yin takarar sa ba tare da kaucewa don Lawan ya samu damar takarar ba.
Tuni magoya bayan Machina su ka ce zamanin Lawan na more kujerar majalisa ya kare don ya kasance a majalisar shekaru 23 da su ka wuce.
Magoya bayan na gangami da nuna su sam ba za su janye don Lawan ya samu gurbin takara ba.
Hukumar zabe ta tsayar da ranar 17 ga watan nan ta zama ranar karshe ta mika jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyu na shugaban kasa da majalisar dokokin taraiya.