• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN LEKEN ASIRI NA MASAR YA SAUKA A GAZA

Shugaban hukumar leken asiri na Masar Abbas Kamel ya sauka a birnin Gaza na Palasdinawa don tattaunawa da Hamas kan yanda Isra’ila ta yi kwana 11 ta na ruwan wuta a burnin.

Kamel ya fito daga garin Ramallah ya shigo Gaza ta mashigar Erez inda jami’an Hamas karkashin jagoran ta na siyasa Yahya Sinwar.

Kamel ya zo Gaza don cigaba da tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya da Masar ta jagoranta don kawo karshen zubar da jini daga yakin.

Masar na son tabbatar da zaman lafiya na tsawon lokaci da samun sake gina Gaza da boma-boman Isra’ila su ka ruguza sassan ta da dama.

Musayar fursunoni tsakanin Hamas da Yahudawa na daga bayanan da a ka tattauna.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.