• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN LEBANON YA YI GUGAR ZANA GA KUNGIYAR HEZBOLLAH

Shugaban Lebanon Michel Aoun ya yi gugar zana ga kungiyar Hezbollah ta ‘yan shia kan lamuran tsaron kasa duk da bai ambaci kungiyar da sunan jam’iyyar siyasa ba.
A jawabi ta kafar talabijin, Aoun ya ce harkokin tsaron cikin kasa na tafiya ne da sojoji da masu turjiya amma duk abun da za a yi matsaya ta na hannun gwamnatin kasa.
Michel Aoun ya ce lalle hakkin gwamnati ne kula da tsaro, don haka sai ta kawar da duk wasu masu kawo zagon kasa.
A jawabin Aoun ya nuna muhimmancin kulla danganta tsakanin kasar da sauran kasashen larabawa, ya na mai cewa ba daidai ne kasar ta rika shiga abun da bai shafe ta ba.
Ba mamaki Aoun na nufin batutuwa irin na yakin da rundunar larabawa ke yi da ‘yan tawayen houthi da ‘yan Hezbollah ke caccaka ko ma su ka shigo Yaman sun a koyawa ‘yan tawaye dabarun harba makamai masu linzami ko jirgi marar matuki.
Dangatanka tsakanin jam’iyyar Aoun da ‘yan Hezbollah ta shiga ragaita.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABAN LEBANON YA YI GUGAR ZANA GA KUNGIYAR HEZBOLLAH”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *