• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN LEBANON MICHEL AOUN YA NUNA FARGABAR KASAR NA IYA DAIDAICEWA MATUKAR BA A KAFA SABUWAR GWAMNATI BA

Shugaban Lebanon Michel Aoun ya nuna fargabar matukar ba a samu nasarar kafa sabuwar gwamnati ba a kasar, to kasar za ta iya shiga mummunan rudani. Aoun a jawabin da a ka yada ta kafar talabijin, ya ce za a iya samun mu’ujizar kafa gwamnati da za ta kawar da ra’ayoyin bangarorin siyasar kasar. Sabon firaminista Mustapha Adib ya bukaci hadin kai daga dukkan ‘yan siyasar kasar wajen kafa gwamnatin kwararru da za ta tsamo kasar daga karin tabarbarewar tattalin arziki. Lebanon dai na da tsarin shugaban kasa kan zama kirista ne, firaminista musulmi dan ahlussunnah sai kuma shugaban majalisa dan shi’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.