Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Wabba ya jagoranci zanga-zanga a Kaduna don nuna rashin amincewa da muradin gwamnatin jihar na rage ma’aikata.
Gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai ya ce ma’aikata na lashe akasarin kudin jihar don haka rage su zai ba wa gwamnatin rarar kudi da za ta rika amfani da su wajen aiyuka.
Tuni dama kungiyar kwadagon ta aiyana fara yajin aiki a jihar duk da barazanar gwamnati ta daukar matakai masu tsauri kan ma’aikatan da su ka ki zuwa aiki.
Kazalika gwamnatin Kaduna na zaiyana Wabba a matsayin mai neman tada fitina don haka ta ke bukatar a cafke shi don fuskantar hushin gwamnati.
An ga faifan bidiyo mai nuna ‘yan sanda na harba borkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀