• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN HUKUMAR SHIGE DA FICE NA NAJERIYA MUHAMMAD BABANDEDE YA KAMMALA WA’ADI

Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya kammala wa’adin aiki inda ya mika ragama a helkwatar hukumar da ke daf da filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Muhammad Babandede ya hau mukamin shugaban hukumar a 2016 yayin da shugaba Buhari ya nada shi.

Babandede daga jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ya hau babban mukamin bayan rike mukamai a matakai daban-daban a hukumar a ciki da wajen Najeriya.

Cikin manyan aiyukan da ya aiwatar har da kafa cibiyar fasaha ta samun bayanan sirri don taimakawa lamuran tsaro.

Hakanan Babandede ya bullo da tsarin da bako ka iya nema ya kuma samu VISA ta Najeriya da zarar ya sauka a filin jirgin sama.

Yayin da za a tuna Babandede da yanda ya taimaka a ka gina katafaren masallaci daura kuma da babbar majami’a a helkwatar hukumar, ya na daga mutanen da su ka iya tafiyar jami’ai mai burgewa ta hanyar taku kwas-kwas da jefa hannu gefe-da-gefe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *