• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN GWAMNATIN JAMUS YA SAUKA KYIV DON SA BAKI GA DAKATAR DA SHIRIN MAMAYE UKRAINE

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sauka a babban birnin kasar Ukraine wato Kyiv don sa baki ga neman dakatar da mamaye kasar daga kasar Rasha.
Bayan kammala ganawa a Kyiv, Scholz zai shiga babban birnin kasar Rasha, Masko don ganawa da hukumomin kasar da jan hankalin su ga fasa mamaye Ukraine.
Scholz na yunkurin dakatar da fitinar da a ke ganin za ta iya fin zamanin yakin cacar baki a yankin, matukar Rasha ta mamaye Ukraine.
Gabanin ziyarar, shugaban Faransa Emmanuel Macron ma ya dau irin matakin don dakatar da babbar fitina a yankin gabashin turai.
Tuni shugaban Rasha Vladimir Putin ya zagaye Ukraine da fiye da sojoji dubu 100 da ke cikin shirin ko-ta-kwana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABAN GWAMNATIN JAMUS YA SAUKA KYIV DON SA BAKI GA DAKATAR DA SHIRIN MAMAYE UKRAINE”
  1. Normally I don’t read article on blogs, however I would like to say that this write-up very pressured me to check
    out and do it! Your writing style has been amazed me. Thanks, very great post.

Leave a Reply

Your email address will not be published.