• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN DAESH YA KASHE KAN SA BIYO BAYAN HARIN AMURKA A TUNGAR SA DA KE SHAM

ByNoblen

Feb 4, 2022

Shugaban Daesh ya hallaka kan sa biyo bayan harin da Amurka ta kai kan tungar sa a yankin Idlib na kasar Sham.
Shugaban Amurka Joe Biden shi ya baiyana haka a jawabin da ya yi da a ka yayata ta kafar talabijin.
Shugaban na Daesh Abu Ibrahim Al-Hashimi Al-Qurashi ya zama shugaban Daesh a 2019 bayan hallaka tsohon shugaban Daesh din Abu Bakr Al-Baghdadi a nan yankin na Idlib.
Biden ya ce Amurka ta raba duniya da daya daga gaggan masu aikata ta’addanci a duniya.
Joe Biden ya ce ya umurci dakarun kasa su jagoranci kai samame kan gidan da Al-Qqurashi ya ke ciki don rage yawan mutane da za a kashe. Amma Al-qurashi sai ya tada bom a hawan bene da ya ke inda ya mutu tare da dama daga iyalin sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.