• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN AMURKA TRUMP YA UMURCI YAWANCIN SOJOJIN AMURKA SU FICE DAGA SOMALIYA

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umurnin akasarin sojojin Amurka da ke Somaliya su fice daga kasar.

Cibiyar tsaron Amurka Pentagon ta ba da wannan sanarwa bisa muradin shugaba Trump na janye sojojin Amurka daga aikin yaki da ta’addanci a ketare.

A yanzu haka akwai sojojin Amurka 700 a Somaliya da ke ba da shawara ga hukumomin kasar hanyoyin rage kalubalen ‘yan Alshabab da ke da manufa daya da kungiyar Alka’ida ta Osama bin Laden.

Janye dakarun zai faru ne a farkon shekarar badi yayin da a ke ganin shugaba Trump zai mika ragama ga Joe Biden.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “SHUGABAN AMURKA TRUMP YA UMURCI YAWANCIN SOJOJIN AMURKA SU FICE DAGA SOMALIYA”
  1. Excellent article! We will be linking to this particularly great article on our website.

    Keep up the good writing.

  2. Hello to every body, it’s my first pay a visit of this web site; this weblog includes remarkable and actually excellent information in favor of readers.

  3. Hi, i feel that i noticed you visited my weblog thus i came to return the want?.I am trying to to find issues to improve my site!I guess its
    adequate to use some of your ideas!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.