• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABAN AFGHANISAN NA GWAMNATIN TALIBAN MULLAH BARADAR YA SAUKA A KANDAHAR

Sabon shugaban Afghanistan Mullah Baradar ya sauka a birnin Kandahar daga Katar inda tun a Febreru ya jagoranci zaman sulhu da tsohuwar gwamnatin ta Ashraf Ghani da ke samun kariyar Amurka.

Kandahar dai nan ne cibiyar mulkin Taliban duk da yanzu hankali ya koma kan birnin Kabul.

Kakakin Taliban Zabibullah Mujahid ya ba da tabbacin nuna sassaucin Taliban ga al’ummar kasar amma kowa zai yi harkar sa bisa koyarwar Islama.

Mujahid ya ce za a ba wa mata damar yin aiki da shiga lamuran kasa bisa tanadin shari’ar Islama.

Taliban ta ce ba za ta dauki matakin ramuwar gaiya ga sojojin tsohuwar gwamnati da su ka yi aiki da Amurkawa ba.

Saudiyya ta yi alwashin Mara baya ga al’ummar Afghsnistan karkashin sabuwar gwamnatin da ke cewa ba ta son cigaba da kiyaiya da kowace kasa.

Amurka ta cigaba gaba da jigilar jami’an ta bayan samun cikas na mutanen Afghsnistan da su ka auka filin jirgin don neman arcewa daga kasar da gudun ramuwar gaiya daga Taliban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.