• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI ZAI SAUKA A ABIDJAN NA COTE D’IVOIRE DON TARON YAKI DA HAMADA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sauka a babban birnin kasar Cote d’ivoire wato Abidjan don halartar taron yaki da hamada.

Taron na 15 na matakan kasashen duniya kan barazanar hamada, zai samu halartar kasashe kasashe daban-daban don tattaunawa kan wannan muhimmin lamari a rayuwar dan-adam.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya fitar sanarwar tafiyar shugaban taron wanda ya ke da zummar kare kasa don amfanin al’ummar yanzu da wadanda ke zuwa nan gaba.

Kasashen yankin Sahel na Afurka na fama da sauyin yanayi don yanda dalilai kan sa sare bishiyoyi da hakan ke maida dazuka su zama tamkar an share sai tarin yashi da kura.

Masana na kawo zabin aiki da makamashi musamman wajen girki don rage sare bishiyoyi

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI ZAI SAUKA A ABIDJAN NA COTE D’IVOIRE DON TARON YAKI DA HAMADA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.