• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI ZAI NUFI LONDON DON DUBA LAFIYAR SA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a talatar nan don shiga London inda za a duba lafiyar sa.

Kakakin shugaban Femi Adeshina ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar daga fadar Aso Rock.

Sanarwar ta baiyana cewa shugaban zai dawo nan a mako biyu wato kwana 14 bayan duna lafiyar ta sa.

Dama can shugaba Buhari kan karbi magani a London don nan ne ke da kwararrun likitocin da ke duba shi.

Dangin sa ma kamar Mallam Mamman Daura kan tafi London don neman magani.

A baya dai shugaba ya taba shafe wajen wata uku a London inda jama’a su ka yi ta taya shi da addu’a har ya samu sauki ya dawo Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *