• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI ZAI KOMA GONA BAYAN KAMMALA WA’ADIN MULKIN SA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai koma gona ya cigaba da aiki bayan kammala wa’adin mulkin sa a 2023.
Shugaban na magana ne a ziyarar aiki kasar Turkiyya a sakon murnar maulidin san a  cika shekara 79 a duniya.
Muhammadu Buhari wanda ya sauka a Turkiyya don taro na 3 na hadin guiwar kasashen Afurka da Turkiyya kan tattalin arziki, ya ce zai cigaba da yin iya bakin kokarin sa a sauran wa’adin mulki da ya rage ma sa.
Shugaban ya godewa Allah da ya nuna ma sa wannan lokaci, ya na mai cewa ya dauka tafiya Turkiyya da ya yi, za ta say a zullewa murnar ranar haihuwar sa amma sai da a ka gudanar da bukin yanka alkaki na murnar da ke lullube da kalolin tutar Najeriya

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI ZAI KOMA GONA BAYAN KAMMALA WA’ADIN MULKIN SA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *