• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI ZAI KADDAMAR DA FARA AIKI DA E-NAIRA

ByYusuf Yau

Oct 25, 2021

A litinin din nan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da shirin fara aiki da Nairar yanar gizo da babban banki CBN ya bullo da tsarin.
Daraktan sadarwa na bankin Osita Nwanisobi ya baiyana hakan a sanarwa da ta baiyana cewa shugaban zai kaddamar Naira yanar gizo wato “eNiara” a fadar Aso Rock.
Nwanisobi ya ce hakan sakamakon bincike ne na tsawon shekaru don saukaka hada-hadar kudi da cinikaiya ta hanya mai sauki.
Babban bankin CBN ya ce darajar eNaira daidai ne da takardar Niara da mutum ke rike da ita ko wacce ta ke aljihun sa, bambanci dai wannan kudi ne da za a rika kashewa ta na’ura ba tare da amfani da takarda ba.
Hakan na nuna fadada tsarin bankin ne na rage rike takardun kudi da komawa huldar kudi ta hanyar na’urorin yanar gizo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI ZAI KADDAMAR DA FARA AIKI DA E-NAIRA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.