• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI ZAI BAIYANA GABAN MAJALISAR DOKOKIN NAJERIYA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai baiyana gaban hadedden zaman majalisar dattawa da wakilai don gabatar da jawabi a ranar alhamis din nan mai zuwa.

A na sa ran shugaban zai zo don yin jawabi ne kan lamuran kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara musamman a jihohin arewacin kasar.

An samu tabbacin baiyanar shugaban daga mai taimaka ma sa kan yanar gizo Lauretta Onochie a shafin ta na twitter.

Tun farko majalisar wakilai ta bukaci shugaban ya baiyana gaban ta don amsa tambayoyi kan lamuran na tsaro.

An samu barkewar muhawara tsakanin ‘yan PDP mai adawa a majalisar wakilai da ke bukatar shugaban ya yi murabus da ‘yan APC da suka yi fatali da bukatar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “SHUGABA BUHARI ZAI BAIYANA GABAN MAJALISAR DOKOKIN NAJERIYA”
  1. Wow, fantastic blog structure! How lengthy have you ever been running
    a blog for? you made running a blog glance easy.
    The whole glance of your web site is magnificent, let alone the content!

  2. I just could not depart your web site prior to suggesting that I really enjoyed the usual info
    an individual provide to your visitors? Is going to be back steadily to inspect
    new posts

Leave a Reply

Your email address will not be published.