Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kamo hanyar dawowa Abuja daga Turkiyya, ya jagoranci wani taro ta na’ura kan lamuran tsaro.
Shugaban wanda ya halarci taro na uku na tattalin arzikin Afurka da hadin guiwar Turkiyya, ya nufo gida da zummar sake dabaru kan tabarbarewar tsaro musamman hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma.
Taron ya samu halartar mataimakin sa Yemi Osinbajo da sauran jagororin cibiyoyin tsaro.
Zuwa rubuta wannan labari ba rahoton bayan taron kan irin abubuwan da za a sa ran gani in shugaban ya dawo fadar Aso Rock.
In za a tuna shugaban ya ce zai yi iya kokarin sa a sauran wa’adin da ya rage ma sa zuwa mayun 2023 daga nan zai koma gonar sa a Daura jihar Katsina.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Keep this going please, great job!