• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA ZIYARCI JIHAR IMO DA TA FI TSANANTAR NEMAN RABA NAJERIYA

Shugaban Najeriay Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Imo da ta zama mafi tsanantar kashe-kashe don neman raba Najeriya da kafa kasar Biyafara.

Shugaban ya ziyarci jihar mai yawan masu hallaka ‘yan arewa; bisa gaiyatar gwamnan jihar Hope Uzodinma.

Ziyarar ta kasance cikin tsauraran matakan tsaro don yanda jihar ta ke da miyagun iri masu daukar gwamnatin APC a matsayin abokiyar gaba.

Shugaban ya yi amfani da ziyarar wajen kaddamar da wasu aiyuka da gwamnan ya aiwatar tun bayan zaman sa gwamna sanadiyyar hukuncin kotun koli da ya ture tsohon gwamna Emeka Ihedioha na PDP.

Gwamnan Ebonyi Dave Umahi da dan takarar APC a zaben gwamnan Anambra Andy Uba na daga cikin wadanda su ka tarbi shugaban.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI YA ZIYARCI JIHAR IMO DA TA FI TSANANTAR NEMAN RABA NAJERIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *