• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA SAMU CIKAKKIYAR KARIYA DAGA KORONA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu cikakkiyar kariya daga annobar korona bayan yin rufakafi zagaye na biyu.

An yi wa shugaban allurar a gidan sa na hukuma a fadar Aso Rock.

Bisa ka’ida a kan yo allurar zagaye na farko da na biyu ne da tazarar lokaci a tsakani da hakan ke nuna an samu rigakafi ya fi magani.

Hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya na nuna a na gab da kammala rigakafi ga rukuni na farko na mutanen Najeriya cikin shirin samar da rigakafin Astra Zaneca karkashin tallafin COVAX ga kasahe masu tasowa.

Duk yanda manyan jami’an gwamnati su ka karbi rigakafin, akasarin ‘yan Najeriya na nuna dari-dari kan allurar da ba sa marmarin ta iso wajen su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.