• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA NADA DOYIN SALAMI A MATSAYIN MAI BA DA SHAWARA KAN TATTALIN ARZIKI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Doyin Salami a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki.
Nadin Salami na kunshe a sanarwa da kakakin shugaba Buhari Mr.Femi Adeshina ya fitar.
Kafin nadin na sa Farfesa Salami ne shugaban cibiyar ba da shawara kan tattalin arziki ta shugaban kasa.
Aikin Salami zai zama tsara manufofin tattalin arziki na cikin gida, zuba ido kan lamuran tattalin arziki duniya da kuma bullo da hanyoyin samar da aiyukan yi ga dimbin ‘yan kasa.
Salami ya taba zama a kwamitin tsare-tsaren kudi na babban bankin Najeriya CBN

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *