• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA NADA BABAGANA KINGIBE A MATSAYIN JAKADAN CHADI DA TAFKIN CHADI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada ambasada Baba Gana Kingibe matsayin jakadan musamman na Najeriya a Chadi da kuma lamuran kasashen yankin tafkin Chadi don kula da lamuran tsaro da dimokradiyya.

A sanarwa daga sakataren gwamnatin Boss Mustapha, ta ce Kingibe zai kula da dawo da mulkin dimokradiyya daga na soja a Chadi.

Hakanan jakadan zai rika tsara hada kan kasashen ga lamuran tsaro a madadin matsayin Najeriya mai muhimmanci a yankin.

Kingibe wanda marigayi shugaba ‘Yar’adua ya kwabe daga matsayin sakataren gwamnati ya nads Yayale Ahmed, ya zama mukarrabin shugaba Buhari da sauran manyan masu ba da shawara ga gwamnatin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.