• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA KI SANYA HANNU KAN SABUWAR DOKAR ZABE

ByNoblen

Dec 22, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu kan sabuwar dokar zabe bayan kwashe wata daya da mika ma sa kudurin dokar da majalisa ta amince da shi.
Wannan dai ba zai zama abun mamaki don shugaban gabanin zaben 2019 ma ya ki amincewa da kudurin dokar zabe da ya kunshi sauya jerin lokutan zabe.
Sabuwar dokar da shugaban ya kaucewa amincewa da ita ta kunshi gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu ta hanyar ‘yar tinke da kuma tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura.
Shugaban ya baiyana kin amincewa da sanya hannun ta hanyar doguwar wasika da ya aikawa majalisar dattawa da kuma majalisar wakilai.
Muhammadu Buhari ya ba da dalilin jingine kudurin da ya hada da kalubalen tsaro, kashe makudan da ma sarkakiyar sharia.
Shugaban ya ce ya samu shawarwai daga ma’aikatu da sassan gwamnati gabanin baiyana matsayar kin amincewa da sanya hannun.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *