• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA KARAWA BABBAN HAFSAN SOJAN KASA GIRMA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karawa babban hafsan sojan kasa Manjo Janar Farouk Yahaya girma zuwa Laftanar Janaral.

Shugaban ya makalawa Yahaya alamar karin girman a fadar Aso Rock gabanin taron mako na majalisar zartarwa.

Wannan ya nuna sabon babban hafsan ya shiga mataki na kusa da na karshe mafi daraja a soja wato Janaral. Duk da haka akwai wani matsayin da ba a samu a Najeriya ba wato FIL MASHAL.

Zamanin tsohon shugaba Ibrahim Babangida ya so ya zama Fil Mashal amma bai yi hakan ba har ya bar mulki a 1993.

Shi kan sa shugaba Buhari ya bar soja a matsayin Manjo Janar ne wato wannan mukamin da Yahaya ke kai kafin samun karin girma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *