• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA KADDAMAR DA NAIRAR YANAR GIZO WATO eNaira

ByYusuf Yau

Oct 27, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aiki da Nairar na’ura wato eNaira da ya nuna tsarin ya fara aiki.

An yi taron kaddamarwar a fadar Aso Rock inda gwamnan babban banki Godwin Emefiele ya halarta.
Tuni babban bankin CBN a takaice ya sanya bayanan yanda za a shiga tsarin hakanan akwai mahanjar shiga a shafin sauke manhaja na waya wato “play store.”

Yayin shiga za a bukaci mutum ya rubuta suna, lambobin shaidar daukar yatsun hannu da sauran su don tabbatar da tsaro.

Bankin ya bukaci masu mu’amala da bankuna su karbi sabon tsarin hannu biyu.

Najeriya na daga cikin kasashe kalilan da su ka shiga wannan tsari na eNaira.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.