• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA JANYE TAFIYA LONDON DON NEMAN MAGANI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya janye tafiyar da ya sanar zai yi zuwa London na Burtaniya don duba likita a jumma’ar nan

Kakakin shugaban Femi Adeshina wanda ya fitar da sanarwar shirin tafiyar a ranar alhamis ya sake fitar da sanarwar janye tafiyar zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba.

Kusan za a iya cewa wannan zai zama karo na farko da shugaban ya sanar da yin tafiya ganin likita amma ya janye.

Ba wani dalilin da fadar shugaban ta bayar kan janye wannan tafiya ta ganin likita.

A zahiri dai shugaban ya zabi tafiya Burtaniya a duk lokacin da za a binciki lamarin lafiyar sa kuma labaru sun nuna dama can ya kan je tun kafin ya lashe zabe a 2015.

A gefe guda masu adawa da shugaban karkashin jagorancin mai taimakawa tsohon shugaba Jonathan wato Reo Omokri, sun ce sun shirya zanga-zanga ta adawa da tafiyar shugaban waje don neman magani.

Su Omokri sun ce barazanar shirin zanga-zangar su ta sa shugaban ya dakatar da tafiyar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.