Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk.
Wannan ganawa ce ta murnar idin babbar sallah da shugaban ya yi a matsayin sa na mai rike da sarautar Bayajidda.
Sarki Umar Farouk ya zaiyana shugaban da mai halayen kwarai kuma kokarin sa ya taimaka wajen hana tabarbarewar lamura a Najeriya.
Sarkin ya yi fatar samun zaman lafiya da kyautatar lamuran tsaro.
An ga dan shugaban Yusuf tare da sarkin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀