• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA GANA DA GWAMNONIN AREWA KAN TSARO

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da kungiyar gwamnonin arewa a fadar Aso Rock kan tsaron yankin.

Shugaban ya gana da gwamnonin bisa jagorancin shugaban kungiyar su, gwamna Simon Lalong na jihar Filato.

Ganawar ta ba da dama ga gwamnonin daya bayan daya sun yi bayanin halin da jihohin su ke ciki kan lamuran tsaro da bukatar irin dauki da su ke yi daga gwamnatin taraiya.

Rahoto ya nuna cewa shugaban ya yi alwashin daukar matakin gamawa da miyagun iri da ke addabar yankin arewacin Najeriya kama daga ‘yan boko haram, masu satar mutane da sauran ‘yan bindiga dadi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *