• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA FARA AIYUKAN NUNA BAN KWANA DA MULKI

ByNoblen

Jun 16, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na wasu kalamai da aiyuka da ke nuna shirin sa yin ban kwana da mulki a 2023.

A tsarin mulki dai shugaban zai sauka daga mulki ne a ranar 29 ga mayu na badi, inda a yanzu tuni ya kwana 14 a cikin kimanin 363 da su ka saura ma sa kan karaga.

Duk inda shugaban ya samu damar jawabi, yak an kawo cewa zai yi kokarin ganin an gudanar da zabe na adalci.

Shugaban kan nuna wasu na da saurin mantuwa kan yanda ya ce gwamnatin sa ta samu kasar a dagule amma yanzu ya daidaita ta, ta yi dama-dama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.