• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA DIRA JIHAR IMO (Hotuna)

ByNoblen

Sep 14, 2022

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Imo inda ya kai ziyarar aiki ta kwana daya domin kaddamar da ayyukan gwamnatin Gwamna Hope Uzodimma ta kammala.

Shugaban ya sauka filin jirgin saman Sam Mbakwe Cargo da misalin karfe 11 na safiyar ranar Talata inda Gwamna Uzodimma da sauran shugabannin jihar suka tarbe shi.

Haka kuma Buhari ya samu tarba daga dimbin jama’a a filin jirgin inda akasarin maza sun sanya jajayen hula da fararen kaya. Akwai kuma mata sanye da kayan gargajiya suna rawa a kan kwalta yayin da shugaban ya isa jihar Imo.

Shugaban ya kaddamar da hanyoyin Okigwe da Orlu da kuma ginin majalisar dokokin da aka gyara a Owerri.

Shugaban kasa Muhammadu tare da Gwamna Hope Uzodimma sun kaddamar da aikin titin kilomita 56 daga Owerri zuwa Okigwe a Amaraku.

Ziyarar ta ranar Talata na zuwa ne kimanin shekara guda bayan da shugaban Najeriyar ya zo jihar domin kaddamar da ayyuka da tattaunawa da shugabannin Igbo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
8 thoughts on “SHUGABA BUHARI YA DIRA JIHAR IMO (Hotuna)”
  1. Wow! This blog looks exactly like my old one! It’s on a completely different subject but it has pretty much the same layout and design. Excellent choice of colors!

Leave a Reply

Your email address will not be published.