Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bude tambarin alamun cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci da zai cika a daya ga watan gobe.
Najeriya dai ta samu ‘yanci daga Burtaniya a 1960 inda gwamnatin shugaban kasa da firaminista ta kawo ga karshe da juyin mulkin kisan gilla a 1966 inda masu juyin mulkin su ka kashe Sir. Abubakar Tafawa Balewa, Sir. Ahmadu Bello da Ladoke Akintola.
Shugaba Buhari ya bude tambarin ne gabanin taron majalisar zartarwa da a ka saba gabatarwa a ranakun Laraba.
Cika shekaru 60 da samun ‘yanci ya sanya Najeriya ta yi canzaras a shugabancin sojoji da farar hula inda in an yi nazari za a ga kowa ya samu shekaru 30.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀