• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI YA BA DA UMURNIN MURKUSHE BARAYI KAN HANYAR ABUJA ZUWA KADUNA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 26, 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin jami’an tsaro su murkushe barayin daji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wannan ya fito ne ta bakin ministan cikin gida Rauf Aregbesola bayan taron majalisar tsaro da shugaban ya jagoranta.
Aregbesola ya ce shugaban ya ba wa jami’an umurnin su dukufa wajen magance matsalar barayin kan babbar hanyar da sauran sassan da a ke samun kalubalen.
Manema labaru sun nemi tabbaci daga ministan cewa an ambaci hanyar Abuja zuwa Kaduna?, Aregbesola ya amsa da hakika an ambata kuma tuni jami’an ‘yan sanda na zuba ido kan hanyar don tsaron lafiya da dukiyar jama’a.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI YA BA DA UMURNIN MURKUSHE BARAYI KAN HANYAR ABUJA ZUWA KADUNA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *