• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI KA IYA TURA SABON KUDURIN DOKAR ALBARKATUN FETUR GABAN MAJALISAR DOKOKIN TARAIYA

A na sa ran a makon gobe shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tura sabon kudurin dokar kula da sarrafa albarkatun man fetur ga majalsar dokokin taraiya. Dama an dade a na muhawara kan wannan kudurin inda a yanzu don samun faduwar farashin fetur, kudurin ya sake farfadowa.

Kudurin dai zai rage irin haraji ko cajin da kamfanonin hakar mai ke yi wajen gudanar da aikin su da kuma tilasta mu su taimkawa yankunan da su ke hakar man. Hakanan labarin da ya samo asali daga kamfanin dillancin labaru na REUTERS, na nuna kudurin zai shafi kula da lafiyar muhalli da kuma sanya tsarin nemo man fetur da iskar gas.

Dokar man fetur dai ta tsufa don wacce a ke aiki da ita tun ta shekarun 1960 ne. Ba a sani ba ko kudurin ya shafi batun tura kudi mai tsoka da a ke yi ga jihohin da ke da albarkar fetur ko kuwa a’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHUGABA BUHARI KA IYA TURA SABON KUDURIN DOKAR ALBARKATUN FETUR GABAN MAJALISAR DOKOKIN TARAIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.