• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHUGABA BUHARI BAI HALARCI JANA’IZAR JANAR ATTAHIRU BA DON BA YA SON TAKURAWA JAMA’A-GARBA SHEHU

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ce shugaban bai samu halartar jana’izar babban hafsan rundunar sojan kasan ba don ba ya son takurawa jama’a a cikin gari.

Garba Shehu da ya ke amsa tambayoyin gidan talabijin na Arise, ya ce kaucewa takurawa jama’a ya sa shugaban ya ke sallar jumma’a a masallacin fadar gwamnati maimakon ya fito waje har jami’an tsaro su rika kuntatawa jama’a.

Da a ka tambaye shi batun nada sabon babban hafsa, Shehu ya ce wannan hurumin shugaban kasa kuma zai nada wanda ya dace.

Rashin halartar jana’izar da shugaban bai yi ba, ya haddasa muhawara mai zafi a kafafen sadarwar yanar gizo na nuna rashin jin dadin yin hakan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.