• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHIRYE-SHIRYE SUN KAMMALA WAJEN AZA HARSASHIN GINA JAMI’AR ASSALAM A YANKIN MASARAUTAR HADEJA

Shirye-shirye sun kammala na aza harsashin fara aikin ginin jami’ar ASSALAM a masarautar Hadeja ta jihar Jigawa arewa maso yammacin Najeriya. Wannan jami’a dai ta kungiyar JIBWIS ta AHLUSSUNNAH, na da zummar ba da dama ga dalibai su samu ingantaccen ilimi da zai zi daidai da yanda za su iya samu a kowacce shahararriyar jami’a a duniya.

Tun a watannin baya aka kaddamar da kwamitin aikin jami’ar karkashin manyan farfesoshi bisa jagorancin farfesa Umar Labdo. Shugabancin JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci jama’a su cigaba da ba da gudunmawa don nasarar aikin ya kammala a takadirin lokaci kuma hakan ya zama sadaka mai wanzuwa. Shehin malamin ya yi addu’ar kyakkyawan sakamako ga wadanda su ka cigaba da ba da gudunmawar kudi don wannan aikin. Tuni a ka fara ganin mota mai tambarin jami’ar na zirga-zirga a babban birnin taraiya Abuja don tsare-tsaren fara wannan aiki gadan-gadan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHIRYE-SHIRYE SUN KAMMALA WAJEN AZA HARSASHIN GINA JAMI’AR ASSALAM A YANKIN MASARAUTAR HADEJA”
  1. After ⅼooking οver a few of the articles on your web page, I truly like your technique of writіng a blog.

    I bookmarked itt to my bookmark webpage list and will be checking back in thе near future.
    Ꮲlease check out my ԝeb site ɑs well and tell me your opinion.

    My blog … http://Www.Testtube.Bookmarking.Site/

Leave a Reply

Your email address will not be published.