• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHIRME NE MU DAWO DA TALLAFIN FETUR ALHALI SAUDIYYA NA SAIDA LITA KAN NAIRA 168 -INJI SHUGABA BUHARI

ByNoblen

Oct 2, 2020 , ,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shirme ne a ce Saudiyya na sayar da litar fetur kan Naira 168, sannan Najeriya mai sayarwa kan Naira 161 ta bar tallafin fetur.

Shugaban wanda ya yi amfani da jawabin dimokradiyya wajen isar da sakon dalilan gwamnatin na kara farashin litar fetur, ya buga misalai da kasashe da dama ciki da jamhuriyar Nijar, Ghana da Masar da ya ce duk sun fi Najeriya tsadar litar fetur.

Shugaba Buhari ya caccaki gwamnatocin baya da cewa sun kusa kai Najeriya ga matakin rugujewa, amma gwamnatin sa ta bullo da lamuran tallafawa al’umma da ‘yan kudi kadan da ta ke da su da ba wata gwamnati da ta taba cimma irin nasarar.

Masu sharhi na tuno yanda ‘yan APC da ke mulki yau su ka dinga kushe tsohuwar gwamnatin PDP lokacin kara farashin litar mai musamman a 2012.

Lamarin dai ya nuna tsarin wadanda su ke kan mulki da maganganun su daban da wadanda su ke gwagwarmayar karbar mulkin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “SHIRME NE MU DAWO DA TALLAFIN FETUR ALHALI SAUDIYYA NA SAIDA LITA KAN NAIRA 168 -INJI SHUGABA BUHARI”
  1. It’s really a nice and useful piece of info. I’m
    glad that you just shared this useful information with us.
    Please keep us up to date like this. Thank you for sharing.

  2. Hey there, You have done a great job. I’ll definitely digg it and personally suggest to my friends.
    I am sure they will be benefited from this website.

Leave a Reply

Your email address will not be published.