• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHIRIN MAMAYE UKRAINE-KASASHEN DUNIYA NA BAIYANA SANYA TAKUNKUMI KAN RASHA

ByNoblen

Feb 24, 2022 ,

Kasashen duniya na baiyana shirye-shiryen takunkumin tattalin arziki kan Rasha don matsa ma ta lamba ta janye daga shirin mamaye Ukraine.
Kama daga Japan, Austarilia, zuwa Amurka da ma karin wasu kasashe na yankin Asia na baiyana matakan takunkumi da su ka shirya azawa kan Rasha kama daga na tattalin arziki zuwa na hana zirga-zirga.
Wannan na faruwa ne a yayin da Rasha ta jibge sojoji dubu 150 a sassa uku na Ukraine da kuma shiga yankin ‘yan aware da ke gabashin kasar.
Tuni ma shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince da ‘yancin yankunan ‘yan awaren.
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya caccaki matsayar amincewa da ‘yancin yankin ‘yan awaren Ukraine da Rasha ta yi, ya na mai cewa hakan keta ‘yancin kasar Ukraine da kuma tsarin zaman lafiya.
Zuwa yanzu dai ba tabbacin Rasha za ta fasa matakan da ta ke shirin dauka kan Ukraine don wannan matsin lamba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.