• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHEIKH MUHAMMAD KABIR HARUNA GOMBE YAYI BABBAN RASHI

Allah ya yi wa mahaifiyar babban sakataren JIBWIS Sheikh Kabiru Haruna Gombe, wato Hajiya Fatima Abdullahi Haruna rasuwa bayan fama da gajeruwar jinya.

Hajiya Fatima mai shekaru 75 ita ce ke yi wa shehun malamin addu’a a duk lamuran sa na wa’azin ahlussunnah.
Marigayiyar ta rasu a hannun dan na ta da samun shaidar rayuwa mai albarka.

An yi jana’izar marigayiyar a jumma’ar nan 30 ga watan nan na Oktoba bayan sallar jumma’a a masalalcin jumma’a na Bolari da ke garin Gombe arewa maso gabashin Najeriya.

Tuni kafafen sada zumunta na yanar gizo su ka tumbatsa da ta’aziyyar rasuwar marigayiyar.

Cikin manyan malamai da su ka yi ta’aziyya akwai Sheikh Abdullahi Bala Lau, Dr.Ibrahim Jalo Jalingo, Dr.Mansur Sokoto da sauran mutane da daman gaske.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “SHEIKH MUHAMMAD KABIR HARUNA GOMBE YAYI BABBAN RASHI”
  1. I’m really enjoying the design and layout of your website.
    It’s a very easy on the eyes which makes it much more pleasant for me to come here and visit more often. Did you hire out a designer to create your theme?
    Outstanding work!

  2. Superb post but I was wondering if you could write
    a litte more on this subject? I’d be very grateful if
    you could elaborate a little bit more. Many thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.