• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHEIKH DAHIRU BAUCHI YA JAGORANCI IDI A TALATA DA HAKAN BAI ZO DAIDAI DA UMURNIN SULTAN BA

Shehun Darikar Tijjaniyya Dahiru Bauchi ya jagoranci sallar idin karamar sallah a gidan sa da ke Bauchi da ya saba da umurnin sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na gudanar da sallar a yau alhamis.

Dahiru Bauchi ya ce an ga watan a Gombe, Gadau da kuma Kebbi don haka ya dau matakin bisa ganin mutum biyu ko taron jama’a.

A ka’ida dai Sultan din Daular Sokoto ta Usman Dan Fodio da duk manyan masarautun arewacin Najeriya ke ciki har da Bauchi, shi ke da hakkin fitar da sanarwar ganin wata bayan tara sanarwar da a ka kawo ko kuma yanda watan in ya cika kwana 30.

A alhamis din nan dukkan sarakuna da manyan kungiyoyin Islama ciki da JIBWIS ke gudanar da idin.

Shugaban majalisar malamai na JIBWIS Dr.Ibrahim Jalo Jalingo ya tabbatar da sultan ke da hakkin ba da sanarwar kuma duk wanda ya gudanar da idi ya yi gaban kan sa ne da ya saba da koyarwar Islama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *