Shaharerren malamin Islama Sheikh Abubakar Gero Argungu ya dawo Najeriya bayan samun sauki da Allah ya ba shi a jinyar da ta kai shi kasar Masar.
Sheikh Gero sanye da doguwar jallabiya fara ya ziyarci helkwatar JIBWIS inda ya gana da shugaban kungiyar Imam Abdullahi Bala Lau.
Akalla dai kafin dawowar sa, wasu sun yada jita-jitar rai ya yi halin sa wanda kuma ya zama ba haka ba don alamu a zahiri sun nuna malamin da ya share shekaru goma ya na yada da’awa ta Ahlusunnah zai koma aikin karantarwar da ya saba.
Imam Abdullahi Bala Lau ya nuna farin ciki da saukin da Allah ya ba wa Sheikh Argungu, ya na mai cewa jinya hanya ce ta kankare kurakuran bayin Allah.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀