• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHEHU BUNGUDU DA YA CE BA KOMAWA APC YA KOMA APC

Dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Zamfara Shehu Ahmed Bungudu da ya ce sam ba maganar sauya shekar su zuwa APC daga APC yanzu ya koma APC.

Shehu wanda ke cikin wadanda kotun koli ta ba wa damar zama dan majalisa anadiyyar rushe nasarar APC, ya taba jaddada cewa hatta gwamnan Zamfara Bello Matawalle ba zai koma APC ba amma karshe ya koma.

Bungudu da a ke yi wa taken sarkin fulani ya fito karara ya nuna yanda PDP za ta ci nasara a zaben da a ka gudanar a jihar Edo inda kuma hakan ya faru gwamna Godwin Obaseki ya lashe zaben.

Hakanan ga ma zaben 2023 da bai zo ba, Bungudu ya nuna PDP za ta samu nasara in an duba yanda APC ta kasa cika alkwarin kamfen.

Yau kuma sai a ka ji sunan Bungudu a jerin sunayen ‘yan majalisar wakilan jihar Zamfara da kakakin majalisar wakilan Femi Gbajabiamila ya gabatar a matsayin wadanda su ka jingine PDP su ka shige APC.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “SHEHU BUNGUDU DA YA CE BA KOMAWA APC YA KOMA APC”
  1. If you want to grow your knowledge just keep visiting this web site and be updated with
    the latest information posted here.

  2. I came to this site with the introduction of a friend around me and I was very impressed when I found your writing. I’ll come back often after bookmarking! slotsite

Leave a Reply

Your email address will not be published.