• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHEHBAZ SHERIF YA ZAMA FIRAMINISTAN PAKISTAN

Dan hamaiya a Pakistan Shehbaz Sharif ya zama sabon firaministan Pakistan bayan zaben sa da majalisar dokokin kasar ta yi.
Zaben ya biyo bayan kuri’ar rashin goyon baya ga tsohon firaministan kasar Imran Khan.
Duk da Khan na da goyon bayan soja, masu sharhi na cewa rashin wadatacciyar fahimtar mulkin kasa ya sa goyon bayan sa ya ragu ainun.
Hakanan Khan ya juya akalar huldar arziki daga Amurka zuwa Sin da Rasha.
Magoya bayan Khan sun yi ta murabus daga majalisar inda Khan ya kuduri aniyar sake takara a zabe mai zuwa.
Sabon firaminista Shehbaz kanin tsohon firaministan kasar ne Nawaz Sharif.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SHEHBAZ SHERIF YA ZAMA FIRAMINISTAN PAKISTAN”

Leave a Reply

Your email address will not be published.