• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SHARI’AR KANU SAI 21 GA OKTOBA

ByNoblen

Jul 27, 2021 , , , ,

Alkalin babbar kotun taraiyar Najeriya a Abuja Binta Nyako ta dage sauraron shari’ar jagoran ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu sai 21 ga watan Oktoba.

Ba lallai rashin baiyanar Kanu gaban kotun ya jawo tsaikon shari’ar ba; amma akwai batun fara hutun alkalai na shekara.

Hukumar tsaron farin kaya DSS ba ta kawo Kanu gaban kotun ba duk da jami’an ta sun mamaye kotun da hanyoyin shiga kotun.

Lamarin ya  ba wa mutane mamaki don  yanda a ka tsaurara tsaro alhali ba za a kawo Kanu kotun ba.
Lauyan Kanun Ifeanyi Ejiofor na neman nuna an fice da Kanu daga Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *