Karshe gwamna Ben Ayade na Kuros Riba ya sauya sheka daga jam’iyyar da ta kai shi kujerar gwamna zuwa APC mai mulki a taraiya.
An kwan biyu ana magana a kan shirin sauya shekar ta sa da nuna ba a gudanar da lamura daidai a PDP.
Shugaban riko na APC Mai Mala Buni da tawagar gwamnoni su ka shaida sauya shekar a gidan gwamnatin jihar da ke Kalaba.
Wasu ‘yan PDP sun ce dama Ayade na makarkashiya ga jam’iyyar ta su, don haka rabuwa da shi nasara ce.
Ben Ayade ya lashe zabe a inuwar PDP a 2015 ya sake samun nasara a 2019.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀