• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA ZA TA FARA DAWO DA GUDANAR DA UMRA DAGA RANAR 4 GA WATAN GOBE

ByNoblen

Sep 23, 2020 , , ,

Bayan kara sassauta matakan yaki da cutar annoba, Saudiyya za ta fara dawo da lamuran zuwa umrah daga ranar 4 ga watan gobe inda za a bar kimanin mutum 6,000 daga ‘yan kasa da baki su gudanar da umrar.

Sai a mataki na biyu zuwa ranar 18 ga watan na gobe za’a kara yawan mutanen su kai 15,000 masu umrah inda wadanda za su yi sallah kadai su kai 40,000.

Ranar 1 ga watan Nuwamba za a budewa sauran musulmin duniya damar zuwa don umrah da samun mutum 20,000 masu umrah inda masu sauran lamuran ibada su kai 60,000.

Karshe hakan zai kai ga lokacin da za a bude duk lamura bayan aminta daga cutar annoba. Alhazai za su iya samun zuwa umrar ta shiga shafin yanar gizo mai taken “I’ Tamarna” da ma’aikatar aikin hajji za ta kaddamar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “SAUDIYYA ZA TA FARA DAWO DA GUDANAR DA UMRA DAGA RANAR 4 GA WATAN GOBE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.