• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA ZA TA DAKATAR DA SHIGO DA KAYAN LAMBU DAGA LEBANON

Saudiyya ta ba da sanarwar daukar matakin hana shigo da kayan lambu kasar daga Lebanon don yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Hukumomi a Saudiyya sun yi zargin a kan yi amfani da kayan lambun daga Lebanon wajen boye miyagun kwayoyi a shigo da su Saudiyya ko daga nan a wuce da su wasu kasashe.

Saudiyya ta ce za ta zuba ido kan sauran kayan da a ke kawowa daga Lebanon don gano ko su din ma akwai wannan damuwa ta fataucin kwaya.

Saudiyya ta ce zata bada dama ne kawai Lebanon ta rika shigo da kayan lambu idan ta ba da tabbacin daukar matakin hana cusa kwaya.

Dokar za ta fara aiki daga lahadin nan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.