• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA ZA TA BUDE DAMA GA ‘YAN KASAR TA SU FARA TAFIYE-TAFIYE DAGA 17 GA WATAN NAN

Saudiyya ta sanar da matakin ba da dama ga ‘yan kasar ta su iya tafiya ketare daga ranar 17 ga watan nan.

A wannan lokacin kasar za ta bude dukkan iyakokin ta na sama, kasa da kuma ruwa don tafiye-tafiye.

Duk da haka wadanda su ka samu yin rigakafin korona ne kashi biyu za su samu damar da kuma wadanda su ka samu rigakafin na farko kwana 14 kafin ranar tafiya.

A baya kasar ta jinkirta ba da damar don jinkirin isowar alluran rigakafi.

Duk wannan na nuna irin saukin da a ke samu daga tsauraran matakan yaki da cutar annoba ta korona.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.