• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA TA GARGADI ‘YAR KASAR SU GUJEWA TAFIYA KASASHEN DA TA DAKATAR DA ZUWA

ByNoblen

Jul 28, 2021 , ,

Saudiyya ta gargadi ‘yan kasar ta su gujewa tafiya kasashen da ta dakatar da zirga-zirga zuwa cikin su don gudun kamuwa da cutar korona.

Hukumomi a kasar sun yi gargadin duk wanda ya saba dokar zai fuskanci haramta ma sa tafiya ketare na tsawon shekaru 3.

Saudiyya ta dakatar da ‘yan kasar ta daga tafiya Indunusiya da ke yankin na nahiyar Asiya don yanda cutar ta yi tsanani a yankin.

Hakanan Saudiyya ta dakatar da zuwa Daular Larabawa in ba da shiri na musamman ba.

Kazalika ta dakatar da zuwa Habasha da Vietnam.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.