• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SAUDIYYA TA FITAR JERIN RUKUNIN FARKO NA KWARARRU DA TA BA WA SHAIDAR ZAMA ‘YAN KASA

ByHassan Goma

Nov 13, 2021

Saudiyya ta fitar da jerin sunayen kwararru ‘yan ketare da ta ba wa shaidar zama ‘yan kasa don haka ya karfafawa guiwar kwararru su zuba jarin basirar su a kasar ta larabawa.
Cikin wadanda su ka samu shaidar da gwanin zanen rubutun hannu Mukhtar Alam wanda ke zaiyana a jikin bakar rigar adon dakin Ka’aba wato KISWA.
Sai kuma wani shaharerren masanin tarihi wanda ya yi rubuce-rubuce da dama mai suna Amin Seido.
Mai binciken ilimi Dr. Muhammad Al-Baqai, masanin tarihi Abdulkarim Al-Sammak da mai nishadantarwa Semaan Al-Ani na daga cikin wadanda su ka samu shaidar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *